ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto rahoton yana cewa tattalin arzikin kasar Lebanon ya tsuge da kasha 6.7 a shekara ta 2019, sannan ya kara tsugewa da kasha 20.3 a shekara ta 2020 sannan ana saran zai kara tsugewa a wannan shekara da kasha 10. Banda haka babu wata alamar gyara a cikin lamarin.
Rahoton ya kammala da cewa mummunan shugabanci da cin hanci da rashawa su ne suka jawo matsalolin tattalin arziki wanda kasar Lebanon ta fada ciki. Banda haka gwamnatin kasar Amurka ta dorawa kasar takunkuman tattalin arziki saboda kasar Syria da kungiyar Hizbullah.
342/